Zabura 75
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce.
1 Muna maka godiya, ya Allah,
muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa;
mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.
2 Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci;
ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.
3 Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza,
ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram.
Sela
4 Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’
ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.
5 Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama;
kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”
6 Ba wani daga gabas ko yamma
ko hamada da zai ɗaukaka mutum.
7 Amma Allah ne mai yin shari’a,
yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.
8 A hannun Ubangiji akwai kwaf
cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji;
yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa
su sha shi tas.
9 Game da ni dai, zan furta wannan har abada;
zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,
10 wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye,
amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”