Zabura 76
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce.
1 A cikin Yahuda an san Allah;
sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
2 Tentinsa yana a Salem
mazauninsa yana a Sihiyona.
3 A can ya kakkarya kibiyoyin wuta,
garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi.
Sela
4 Darajarka tana da haske,
fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
5 Jarumawa sun zube kamar ganima
sun yi barcinsu na ƙarshe;
ba ko jarumi guda
da zai iya ɗaga hannuwansa.
6 A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub,
doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
7 Kai kaɗai ne za a ji tsoro.
Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
8 Daga sama ka yi shelar hukunci,
ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
9 sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a,
don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar.
Sela
10 Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo,
waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
11 Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su;
bari dukan ƙasashen maƙwabta
su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
12 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki;
sarakunan duniya suna tsoronsa.